Shugaban Hukumar kula da filaye da Samar da muhalli na Jihar Kaduna Mal. Muhammad Kudu Muhammad shine yayi wannan kiran yayin Taron Hukumar na kasa karo na gomasha biyu da yake gudana a Kaduna.

Ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu lalle ya sanya dokar tabaci akan samar da muhalli a fadin kasar nan don babu wani bangare na kasar da baya fama da daya daga cikin mastalolin da ke damun wannan kasar, kama daga yan bundiga, masu garkuwa da mutane, rikicin manoma da makiyaya na arewaci kenan in kuma ka koma kudanci suma da irin nasu mastalolin kamar stagerun Nija Delta da sauran su to abinda ya rage kurum shine Tinubu ya ayyana dokar ta baci kawai don Samar da muhalli ga yan kasa baki days inji shi.

Kudu ya kara da cewa indai har gwabnatin Jihar borno Zai iya samar da muhalli ga yan Jihar sa wadanda rikincin Boko Haram ya tarwasta su to me zai hana sauran gwabnoni a jihohin su ba za suyi koyi da shi ba.

Manyan baki

Taron dai ya samu halarta masana harkar filaye da kwararru wajen harkar gine gine daga sassa daban daban na jihohin kasar nan kuma suna kan tattaunawa da bada shawarwari kan samar da ingantattun mahallai da kuma daukar matakai kan yawan rushewar gine gine da ake samu akai akai a fadin kasar nan musamman ma a jihohin legas Ibadan da sauran su, Kuma yau ne aka shiga rana ta biyu a taron kuma zai gudana ne na stawon sati guda

Wassu daga cikin mahalarta taron