Shirin Inganta noman zamani  na (Tsarin Cimma Burin Maradun Karni) SDGP da hadin gwiwar ma’aikatar noma ta Jihar Kaduna sun horar da mata da matasa kan dubarun noman zamani.

Gwabnan Kaduna Mal. Uba Sani wanda ya samu wakilcin matemakiyar gwabna wato Hadiza Sabuwa Balarabe ya bayyana cewa wannan horas war tayi daidai da Tsarin gwabnatin sa na bunkasa karkara domin manoma suna karkara ne, kuma noma shine kashin bayan tattalin arzikin mu a wannan Jihar, in ji shi.

Ya kuma kara da cewa wannan tsarin yayi nasara wajen horas da mata da matasa da dama ta yadda hakandin zai bunkasa tattalin arzikin mazauna karkara kuma ya samar wadatattacen kayan amfanin gona musamman kayan miya a cikin kaduna da kewaye.

Mal. Sani Danladi Yadakwari shi ne Sakataren Kungiyar Yan Tumaturi na kasa yayin tattaunawa da manema labarai kira ya yi ga gwabnati da masu ruwa da tsaki kan su samar da Maganin kwari da tsutsa masu lalata amfani musamman tumaturi. Ya kuma kara da cewa karancin tumaturi shi ke kawo tsadar sa, saboda ba isash shen iri kuma ga matsalar tsutsa.

Mal. Sani har ila yau ya yi kira ga manoma da su mai da hankali wajen yin feshi akan amfanin gonar su su kuma hada kai da makwabtan su a gona don in kai ka yi feshe amma makwabcin ka bai yi ba to akwai matsala.

Shi kuma anasa bayanin yayin zantawa da manema labarai daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin Inganta noman zamani wato Mal. Sani Niga Marke godiya yayi ga gwabnatin Jihar Kaduna da duk masu ruwa da tsaki kan wannan shirin na cimma maradun karni, sannan sai yayi kira ga gwabnati da Sarakuna dama masu hannu da shuni da su hada karfi da karfe wajen goya wa wannan shirin baya don jawo matasa cikin tsarin don a rage zaman banza a tsakanin su wanda shi ke kawo rashin tsaro a Arewa da Najeriya baki daya