Yi wa Shugaban Cibiyar yan Jaridu  ta kasa da kasa Mr. Lanre Arogundade  barazanar kama shi ya saba wa doka kuma karya yanci sa ne a matsayin sa na dan kasa, da hana yancin fadin albarkacin bakin dan Adam wadda dokar kasa ta bashi.

Hakan din yana kunshe ne a cikin takardar sanar wa da cibiyar Yan jaridu ta kasa da kasa dake da shelkwata a Ikko (Lagos) ta fitar dauki sa hannun maga takardar Kungiyar Melody Akinjiyan ran 16/4/2024.

Cibiyar ta nuna rashin jin dadin ta kan yadda Jami’an tsaro na farin kaya (DSS) suka ci zarafin Mr. Lanre akan hanyar sa ta zuwa babban taron bayyana yancin dan Adam na yankin Africa da zai gudana a Berlin babban birnin Jamani ran Alhamis 11/04/2024.

Shi dai Mr. Arogundade mutum ne mai son zaman lafiya kuma mai kwato wa talakawa yanci ne, kuma mai son cigaban siyasa ne, fitaccen Dan Jarida ne mai kishin kasa kuma shine shugaban Cibiyar yan Jaridu ta kasa da kasa, ya ma kuma rike Shugaban dalibai na Kasa, ya kuma yi Shugaban Kungiyar yan Jaridu ta kasa na Jihar Lagos.

Mr. Lanre akwai lokacin da ya taba tura sakon kar ta kwana a yanar gizo cewa Jami’an tsaro na farin kaya DSS sun ci zarafin sa har na kusan minti arba’in wai sunan sa ya na cikin wadanda suke nema, bayan kuma shugaban Jami’an tsaro na farin kaya na kasa wato Yusuf Magaji Bichi ya gaya wa Ma’aikatan IPC cewa an cire sunan Mr. Lanre da ga cikin wadanda suke nema, amma duk da haka gashi Jami’an DSS suna musguna masa wadda hakan din sabawa yancin dan Adam ne na walwala da fadin albarkacin baki wadda doka ta tanada.

Don haka Cibiyar yan Jaridu ta kasa da kasa ta yi kira ga Jami’an tsaro na farin kaya DSS da kuma mahukuntan filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas su ja kunnen Ma’aikatan su da Jami’an su da su daina musguna wa Mr. Lanre Arogundade wani ma yayi rawa bare dan makadi.