Malamai daban daban ne suka yi wannan Gargadin a wani taron addu’a na musamman da wata Kungiya mai rajin ci gaban Arewa ta shirya  a Masallacin Dan Fodio dake Unguwar Sanusi a Kaduna.

Alaramma Mal. Alhassan Lamido a jawàbin sa na maraba da baki ya Gargadi al’umma da su koma ga Allah ya hanyar amsa Kiran Allah da ya yi in muna so Allah ya amsa mana addu’in mu domin Allah ya ce “Idan bayi na suka tambaye ka game da ni to ina kusa zan amsa kiran su amma su amsa kira na, in suka roke ni sai in karba musu” sai kuma Alaramman ya yi addu’a jama’ar dake wurin suna cewa amin.

Alaramma Mal. Alhassan Lamido

Shima Ash sheik Halliru maraya dayake nasa jawabin Jan hankalin al’umma ya yi da ayi kokari a tsaftace nema, wato a nemi halas domin Allah baya amsa addu”ar mai cin haram, kuma muyi ta tuba zuwa ga Allah Subhanahu muji tsoron sa, don Allah ya ce “Duk wanda ya ji tsoron Allah to Allah zai sa masa mafita kuma ya arzurta shi ta yadda ba ya tsammani, Shima daga karshe sai ya yi addu’a kamar haka

Ashiek Halliru maraya

Sheik Sanusi Kutama a Madadin Ash sheik Dahiru Bauchi shima a nasa jawabin gargadi ya yi da jan hankalin shugabanni da su kula da nauyin da Allah ya dora musu saboda za a tambaye su gobe kiyama game da talakawan su, kuma ya ja hankalin talakawa da su yi biyayya sannan su mai da al’amarin su zuwa ga Allah, shima sai yayi addu’a.

Sheik Sanusi Kutama yayin zantawa da manema labarai

Shima Mai girma Sarkin Unguwar Sanusi Mal. Sani Sanusi ya yaba wa wannan Kungiyar da ta shirya wannan taron a daidai wannan lokacin sai kuma ya roki Allah Subhanahu da ya amsa duk addu’oin da Malamai sukayi, ya kuma fitar da mu daga halin da muke ciki na rashin tsaro da tsadar rayuwa

Mai girma Sarkin Unguwar Sanusi Mal. Sani Sanusi

Shima yayin da yake tsokaci game da taron Safiyanu Abubakar Dan Tsoho (Turakin Dan Galadiman Zazzau kuma Magajin Rafin Cawai) yaba wa ya yi ga wadanda suka shirya taron da kuma wadanda suka tallafa har aka kai ga cin nasarar wannan taron ya kuma yi addu’a da Allah ya karbi Ibadu da addu’a r da Malamai sukayi

Safiyanu Abubakar Dan Tsoho (Turakin Dan Galadiman Zazzau kuma Magajin Rafin Cawai)

Haj. Hajara Umar Daraktar Kungiyar ta kasa kuma mai kula da walwalar mata yayin zantawa da manema labarai cewa tayi dalilin shirya wannan taron shine don hada kan musulmai na kowane bangare don fitar da yankin Arewacin Najeriya daga halin ni ya su na rashin tsaro, talauci da kuncin rayuwa da ya addabemu, ta kara da cewa wannan din farawa akayi za’a ci gaba da irin wannan taron a wassu wurare  in Allah ya so