Babban matemaki na musamman kan harkokin Addini ga Gwabnan Jihar Kaduna Mal. Uba Sani wato Mal. Abdurrahman Zakariyyah bayan godiya ga Allah madaukakin Sarki sannan ya yaba wa mai girma Gwabnan kan irin gudumowa da goyon baya da yaba su wajen gudanar da wannan musabakar sai yayi kira ga dalibai da su lizimci da’a a yayin musabakar da kuma bayan musabakar.

Ya bayyana hakan ne Jim kadan bayan ganawa da masu ruwa da staki na kwamatin musabakar karatun Alkur’ani na jihar Kaduna karkashin shugabancin Dokta Bello Abdulkadir Salanken Zazzau ayau 21/11/2023 wanda yayi daidai da 7/5/1445 hijiriyyah.

Mal. Abdurrahman ya bayyana wa manema labarai cewa wannan musabakar ita ce ta karo na 38 kuma akwai dalibai masu fafatawa a fannoni daban daban na Alkur’ani daga kananan hukumomi 23 dake fadin Jihar, ya kuma kara da cewa duk wadanda suka samu nasara a wannan musabakar to kuma sune wadanda za su wakilci Jihar a musabaka ta kasa mai zuwa wadda za a yi in Allah ya so Jihar Yobe

Kwamatin musabaka da Alkalai